Buhari ya aika wasika majalisar dattawa, ya sake nada yar Abiola a matsayin daraktar NDIC

Buhari ya aika wasika majalisar dattawa, ya sake nada yar Abiola a matsayin daraktar NDIC

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ga majalisar dattawa domin tabbatar da sabon nadi

- Buhari ya nemi a tabbatar sannan a sabonta nadin Omolola Abiola Edewo a matsayin daraktar hukumar kiyaye ajiyar Jama’a daga barnar bankuna (NDIC)

- Wannan shine karo na biyu da Omolola za ta jagoranci hukumar ta NDIC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ga majalisar dattawa, ya nemi a tabbatar sannan a sabonta nadin Omolola Abiola Edewo a matsayin daraktar hukumar kiyaye ajiyar Jama’a daga barnar bankuna (NDIC).

Abiola Edewo ta kasance babbar yar wanda ya lashe zaben Shugaban kasa a shekarar 1993, ta kuma kasance tsohuwar mamba a majalisar wakilai.

Wannan sabon nadin nata zai zamo karo na biyu kenan da za ta jagorantar hukumar a matsayin darakta.

Buhari ya aika wasika majalisar dattawa, ya sake nada yar Abiola a matsayin daraktar NDIC
Buhari ya aika wasika majalisar dattawa, ya sake nada yar Abiola a matsayin daraktar NDIC
Asali: Depositphotos

Bukatar Shugaban kasar na tattare ne a cikin wata wasika da Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya karanta a zauren majalisa a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu.

Ga yadda wasikar yazo:

“Bukatar tabbatar da kuma sabonta nadin mai girma Omolola Abiola Edewo a matsayin daraktar hukumar kiyaye ajiyar Jama’a daga barnar bankuna.

KU KARANTA KUMA: Zaben Rivers: Wike na gaba da sama da kuri’u 290,000 yayinda INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 15

“Kamar yadda yake a sashi (594) na dokar hukumar kiyaye ajiyar Jama’a daga barnar bankuna, Na rubuta wannan wasika domin majalisar dattawa ta tabbatar da sunan mai girma Omolola Abiola Edewo a karo na biyu kuma na karshe na tsawon shekaru biyar. Akwai takardunta a hade da wasikar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel