Za a gabatar da kudurin magance talauci a Najeriya - Fadar Shugaban Kasa

Za a gabatar da kudurin magance talauci a Najeriya - Fadar Shugaban Kasa

A kokarin da gwamnatin Najeriya ta ke na ganin ta inganta rayuwar talaka, gwamnatin ta bayyana kudurin ta na gabatar da dokar magance talauci ga majalisar dokoki

A jiya ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kammala shirye-shirye don aikawa majalisar dokoki, kudurin da zai kawo hanyar da za a magance talauci a kasar nan.

An bayyana hakan ne jiya Talata 2 ga watan Afrilu a Abuja yayin da kwamitin da aka kafa don magance talauci, wanda suka hada da Sanata Lawal Yahaya Gumau (APC Bauchi), da dan majalisar wakilai, Muhammad Ali Wudil (APC Kano), mai ba wa shugaban kasa shawara ta musamman akan sana'o'i, Maryam Uwais, sun bayyana cewa dokar za ta fara aiki nan ba da dadewa ba, kwamitin ta bayyana cewa a yanzu haka ta na aikin akan yanda za a gabatar da dokar ga majalisa.

Za a gabatar da kudurin magance talauci a Najeriya - Fadar Shugaban Kasa
Za a gabatar da kudurin magance talauci a Najeriya - Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Da take amsa tambayar wani dan majalisar wakilai, Sidi Karasuwa (APC Yobe), Uwais ta ce, "Mun san cewa muna da kyakkyawan kwamiti da zai jajirce wurin ganin wannan kudurin ya tabbata. Mun zo da kudurin wanda muka gama tsara shi da jimawa kafin mu zo mu samu shugabannin biyu.

"Akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu lura da su a cikin kudurin amma muna so, mu gama duk gyare-gyaren da za mu yi kafin mu zo gare ku.

KU KARANTA: Jan hankali: Hukumar NAFDAC na jawo hankalin al'umma akan wani maganin bogi da ya ke yawo cikin al'umma

"A yanzu haka tsarin ciyar da dalibai ya karade jihohi 30, sannan akwai makarantu 56,000 wadanda su ke kan wannan tsarin a fadin kasar nan, ta kara da cewa suna samun taimako daga masu bada agaji irin su Bankin duniya."

A jawabinsa Hon Ali Wudil ya ce kwamitin ta na bukatar ta ga cikakken bayani akan taimakon da aka samu daga Bankin Duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel