Ziyarar Buhari: CAN ta mayarwa NCEF martani

Ziyarar Buhari: CAN ta mayarwa NCEF martani

Kungiyar Kirista ta Najeriya (CAN) tayi watsi da sukar da Kungiyar Dattawan Kirista na Kasa (NCEF) tayi a kan ziyarar da suka kaiwa Shugaba Muhammadu Buhari domin taya shi murnar lashe zabe karo na biyu.

CAN ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ta fitar ta bakin shugaban sashin shari'a da hulda da al'umma na kungiyar, Samuel Kwamkur a ranar Talata.

NCEF ta ce ziyarar da CAN ta kaiwa Buhari alama ce da ke nuna cewa akwai wata alaka mara tsafta da ke tsakanin CAN da jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

A sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, NCEF ta zargi CAN tsunduma kanta cikin siyasa. Ta ce CAN ta dauki hanyar da bai haifawa mabiya addinin Kirista da mai ido ba.

DUBA WANNAN: Namadi Sambo ya goyi bayan Buhari kan tsare-tsaren sa na tattalin arziki

Ziyarar Buhari: CAN ta mayarwa NSCEF martani
Ziyarar Buhari: CAN ta mayarwa NSCEF martani
Asali: Twitter

Amma a martanin da ya mayarwa NCEF, Mr Kwamkur ya ce shugabanin CAN sun ruguza NCEF tun kusan shekara daya da ta gabata saboda haka ba su da ikon yin wata tsokaci a kan harkokin kungiyar ta CAN.

"Babu laifi CAN ta ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari ta taya shi murnar lashe zabe tunda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC ta sanar da cewa shine ya lashe zaben shugabancin kasar na 2019.

"Ina cikin tawagar CAN, ya wuce shekara guda da CAN ta raba jiha da NCEF saboda haka ba dole bane sai an sanar da su idan za a ziyarci shugaban kasa tunda ba su tare da CAN," a cewar Mr Kwamkur.

Mr Kwamkur ya cigaba da cewa, "Mun ziyarci Buhari ne a matsayin mu na kungiya ba wai jam'iyyar siyasa ba kuma bamu da wata jam'iyya ko dan takara da muke goyon baya a matsayin mu na kungiya.

"Muna aiki ne da abinda doka ya tanada kuma tunda INEC a matsayin ta na hukuma da doka ta kafa ta sanar da wanda ya ci zabe, menene dalilin da zai sa ba za mu amince da hakan ba? Idan bamu amince ba wannan ya nuna muna da dan takarar da muke goyon baya kenen."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel