Gogoriyon darewa kujerar Saraki: Ndume ya bayyana kudurorinsa guda 9

Gogoriyon darewa kujerar Saraki: Ndume ya bayyana kudurorinsa guda 9

Guda daga cikin manyan Sanatocin dake gogoriyon gaje kujerar shugaban majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya baje kudurorinsa guda tara a faifai da yake sa ran aiwatar a zamanin majalisa ta tara idan har ya kai bantensa a wannan gwagwarmaya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ndume dai yana wannan takara ne duk kuwa da cewa uwar jam’iyyar APC ta bayyana Sanata Ahmad Lawan a matsayin wanda take muradi ya gaji Saraki, wanda ya samu rashin nasara a kokarinsa na komawa majalisar.

KU KARANTA: Shari’ar Dasuki: Tana kasa tana dabo, Alkali ya sake dage sauraron karar

Gogoriyon darewa kujerar Saraki: Ndume ya bayyana kudurorinsa guda 9
Majalisar dattawa
Asali: Depositphotos

A jawabinsa, Sanata Ndume daya fito daga jahar Borno inda yake wakiltar al’ummar mazabar Bornon ta kudu ya bayyana cewa zai rage ma mukamin shugaban majalisa karsashi, ta hanyar rage duk wasu alfarma da ofishin yake dasu.

Sauran kudurorin Sanata Ndume sun hada da;

- Samar da dokar aikin mazabu, ta yadda ayyukan zasu kasance a bude ba tare da wani boye boye ba

- Tabbatar da cin gashin kan bangaren dokoki

- Tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakanin majalisa da bangaren zartarwa

- Samar da adadin kwanakin tantance mutanen da shugaban kasa ya turo don nadasu mukamai

- Kammala aiki akan kasafin kudin Najeriya cikin kwanaki 90

- Samar da dokokin da zasu lalubo sabbin hanyoyin samun kudaden shiga ga Najeriya

- Tafiyar da majalisar dattawa cikin bin gaskiya da gaskiya, ba tare da nuna wariya ga wani Sanata ba

- Samar da ingantattun dokoki da zasu taimaka ma gwamnatin Buhari wajen cimma muradunta

A yanzu haka dai ana jira a ga wanda zai dare wannan kujera ta shugaban majalisar dattawa tsakanin Ahmad Lawan da Ali Ndume, duba da cewa ba’a sanin maci tuwo sai miya ta kare, amma dai rana ai bata karya, sai dai uwar diya ta ji kunya, kuma dadina da gobe saurin zuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel