Zaben Rivers: Wike na gaba da sama da kuri’u 290,000 yayinda INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 15

Zaben Rivers: Wike na gaba da sama da kuri’u 290,000 yayinda INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 15

- Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamna a jihar Rivers, Nyesom Wike na kan gaba yayinda INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 15

- Wike na da kuri’u 426, 279, yayinda Biokpomabo Awara, dan takarar jam’iyyar African Alliance Congress (AAC), ke da kuri’u 129,855

- Zuwa yanzu dai akwai tazarar kuri'u 296,424 a tsakaninsu

Nyesom Wike, dan takarar gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Rivers, ne kan gaba a sakamakon zaben kananan hukuma 15 da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar.

Hukumar INEC ta fara tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 15 a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu inda Wike ke da kuri’u 426, 279, yayinda Biokpomabo Awara, dan takarar jam’iyyar African Alliance Congress (AAC), ke da kuri’u 129,855, a yanzu haka akwai tazarar kuri’u 296,424.

Zaben Rivers: Wike na gaba da sama da kuri’u 290,000 yayinda INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 15
Zaben Rivers: Wike na gaba da sama da kuri’u 290,000 yayinda INEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 15
Asali: Depositphotos

Obo Effanga, kwamishinan zabe na jihar, yace za a ci gaba da tattara sakamakon zaben da misalin karfe 10 na safiyar ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Kasar Jamus ta taya shugaba Buhari murnar lashe zabe a karo na biyu

Akwai Karin kananan hukumomi biyu da INEC bata riga ta sanar da sakamakonsu ba yayinda za a sake zabe a fadin kananan hukumomi shida a ranar 13 ga watan Afrilu.

Rotimi Amaechi, ministan sufuri, na goyon bayan dan takarar AAC a zaben tun bayan da rikicin cikin gida ya hana jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers tsayar da yan takara a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel