Kasar Jamus ta taya shugaba Buhari murnar lashe zabe a karo na biyu

Kasar Jamus ta taya shugaba Buhari murnar lashe zabe a karo na biyu

- Shugabar kasar Jamus, Angela Merkel ta kira shugaba Buhari a wayar tarho, inda ta taya shi murnar lashe zaben ranar 23 ga watan Fabreru 2019

- Merkel ta sha alwashin ci gaba da hadin guiwa da Nigeria wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro

- Buhari ya godewa shugabar kasar ta Jamus bisa namijin kokarinta na dakile yawaitar shige da fice ba bisa ka'ida ba

Shugabar kasar Jamus, Angela Merkel ta kira shugaban kasa Muhammadu Buhari a wayar tarho, inda ta taya shi murnar lashe zaben ranar 23 ga watan Fabreru 2019, wanda ya bashi damar yin tazarce a karo na biyu.

A cikin wata sanarwa daga Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar watsa labarai a Abuja a ranar Talata, ya ce Merkel ta sha alwashin ci gaba da hadin guiwa da Nigeria wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

KARANTA WANNAN: Saboda rashin takardun sakandire: Kotu ta yi watsi da takarar Adeleke a PDP

Merkel ta kuma sha alwashin bunkasa saka hannun jari da kasuwanci tsakanin Nigeria da Jamus domin dorewar tattalin arzikin kasashen guda biyu.

Sanarwar ta kuma ruwaito shugaban kasa Buhari yana godewa shugabar kasar ta Jamus bisa namijin kokarinta na dakile yawaitar shige da fice ba bisa ka'ida ba, da kuma tallafinta ga masu shige da fice da ke da bukata ta musamman.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel