2019: Jam’iyyar APC da PDP sun dumfari Kotu a Jihar Filato

2019: Jam’iyyar APC da PDP sun dumfari Kotu a Jihar Filato

Jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP mai hamayya za su hadu da juna a gaban kuliya bayan da kowane yake zargin Abokin takarar sa da yin magudi a zaben majalisa da aka yi a jihar Filato.

Kawo yanzu dai Kotun da ke sauraron karar zaben majalisa na jihar Filato ya bada umarni ga hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC da ta fito da kayan aikin da aka yi amfani da su domin PDP ta yi wani binciken kwa-kwaf.

Sakataren yada labarai na PDP a jihar Filato, Abraham Yiljap, ya bayyana cewa Kotu ta bada dama PDP ta duba takardun zaben da INEC ta kawo jihar a lokacin da aka yi zaben jihar wanda APC ce ta sake lashe zaben gwama.

KU KARANTA: 2019: Ganduje ya tafka magudi a zaben Kano – Inji Jagoran APC

Yiljap yayi wannan bayani ne a jiya Ranar Talata 3 ga Watan Afrilu a cikin Garin Jos, bayan Kotun da ke sauraron karar zaben jihar ya fara shirin soma aiki. PDP ta shirya Lauyoyi 10 da za su kare ta a gaban kotun idan an zauna.

Jam’iyyar adawar ta na kalubalantar zaben ‘yan majalisar dokoki na jihar, da kuma ‘yan majalisar wakilan tarayya, da kuma zaben Sanatoci inda ta maka korafi har 10 a gaban Kotu. Ita ma APC tana zargin PDP da yin magudi.

‘Dan takarar gwamna na PDP a zaben jihar watau Sanata Jerry Useni ya yabawa wannan mataki da Kotu ta dauka. Useini ya sha kashi ne a hannun gwamna mai-ci Simon Bako Lalong na jam'iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel