Ban taba ba Mai dakin Shugaban kasa ko NSA wasu kwangila ba – Dokubo

Ban taba ba Mai dakin Shugaban kasa ko NSA wasu kwangila ba – Dokubo

Shugaban tsarin nan na Niger Delta Presidential Amnesty, Farfesa Charles Dokubo, ya bayyama cewa ba su taba bada wata kwangila ga Matar shugaban kasa watau Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ba.

Farfesa Charles Dokubo yayi wannan jawabi ne ta bakin wani Hadimin sa da ke magana a kafafen yada labarai watau Murphy Ganagana. Ganagana yace rade-radin da ke yawo na cewa ana ba Aisha Buhari kwangiloli, ba gaskiya bane.

Shugaban tsarin na Niger Delta Presidential Amnesty mai tallafawa mutanen Yankin Neja-Delta masu arzikin fetur yace Uwargidar shugaban kasar da kuma NSA Babagana Monguno ba su taba amfana da kwangiloli ta hannun su ba.

KU KARANTA: An garzaya da wanda yake hannun EFCC zuwa asibiti bayan ya sume

Ban taba Mai dakin Shugaban kasa ko NSA wasu kwangila ba – Dokubo
An yi watsi da zargin ba Matar Shugaban kasa kwangila
Asali: Twitter

Charles Dokubo ya nemi mutane su yi watsi da wannan karya mara kai da gindi da ake ta faman yadawa domin batawa Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro watau Babagana Monguno da kuma Hajiya Aisha M. Buhari suna.

A jawabin na Murphy Ganagana, ya bayyana cewa wasu ne su ka sha alwashin ganin an yi waje da Farfesa Dokubo daga ofishin sa ko ta wani irin hali. Jawabin ya karasa da cewa wannan shiri da wasu ke yi ba zai ko ina ba, zai rushe.

Kwanakin baya jam’iyyar PDP ta taba zargin cewa gwamnan babban bankin Najeriya na CBN yana ba Uwargidar shugaban kasar da wasu manya a gwamnatin Buhari daloli su na canzawa don a samu riba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel