Kuma dai! An sake garkuwa da mutane 8 a hanyar Kaduna-Abuja

Kuma dai! An sake garkuwa da mutane 8 a hanyar Kaduna-Abuja

Bayan sace mutane 35 a ranar Litinin, masu garkuwa da mutane sun sake kai mumunan hari babban titin Abuja-Kaduna inda suka sace matafiya 8 da suka nufi Abuja.

Wani idon shaida da ya tsallake rijiya da baya ya bayyanawa Daily Nigerian cewa yan bindigan sun bude wuta inda suka tsyaar da motoci kirar Honda da Toyota kuma suka tafi da mutane 8 cikin daji misalin karfe 3:15 na ranar Talata, 2 ga watan Maris, 2019.

Idon shaidan, Lawan Sule, yace: "Daga nesa a kauyen Akilibu da muke kallo, mun ga an shigar da mutane takwas cikin daji. Masu garkuwan basu bata lokaci ba."

Ba'a samu tuntubar kakakin yan sandan jihar, Yakubu Sabo, ba a lokacin da aka kawo wannan rahoto.

A ranar Litinin, an yi awon gaba da kimanin mutane 35 da ke tafiya a wata mota kirar Hilux mai lamba CT 01 AF misalin karfe 6:30 na yamma.

KU KARANTA: Hukuma ta bayyana yan sandan da suka kashe matashi a gida kallon kwallo

Yan bindigan sun kai hari ne kusada kauyen Gidan Busa inda suka bude wuta . Muutum day mai sune Mshelia Suleman, ya jikkata.

Hukumar yan sandan ta tabbatar da wannan hari duk da cewa ta karyata yawan mutanen da aka sace kamar da aka yada a kafanan yada labarai.

A bangare guda, sakamakon hare-hare da garkuwa da mutanen da ya addabi babban hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Birnin gwari, majalisar tsaron jihar Kaduna ta yanke shawaran karfafa sintiri a hanyoyin domin rage hare-haren.

Mun kawo muku rahotannin yadda masu garkuwa da mutane suka dawo hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma hanyar birnin gwari. Tsakanin ranar Lahadi da Litinin kadai, an yi garkuwa da akalla mutane 42.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel