Da na sa ni keya: Ina ba wa iyalan mutanen da na kashe hakuri - Dan kungiyar asiri

Da na sa ni keya: Ina ba wa iyalan mutanen da na kashe hakuri - Dan kungiyar asiri

Wani kasurgumin dan kungiyar asiri da rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kama ya nu na da na sanin shu matuka, in da ya dinga kuka ya na ba wa iyalan mutanen da ya kashe hakuri akan su ya fe mi shi

Wani kasurgumin dan kungiyar asiri, Ogunlaja Elijah, wanda rundunar 'yan sandan jihar Legaas ta ke nema ruwa a jallo ya shiga hannu jiya 2 ga watan Afrilu, in da ya dinga zubar da hawaye cikin da na sa ni akan abubuwan da ya aikata a baya.

Kama wanda ake zargin ya yi wa mutanen unguwar Shomolu/Bariga da ke jihar Legas dadi mutuka, in da su ka bayyana cewa ya zame musu karfen kafa.

Da na sa ni keya: Ina ba wa iyalan mutanen da na kashe hakuri - Dan kungiyar asiri
Da na sa ni keya: Ina ba wa iyalan mutanen da na kashe hakuri - Dan kungiyar asiri
Asali: UGC

A lokacin da ya ke bayanin yanda ya kashe wasu mutane biyu a shekarar da ta gabata, Elijah, wanda aka kama tare da abokanan sana'arsa su biyu, ya bayyana cewa ya shiga kungiyar asiri ne a shekarar 2016, a lokacin da ya je bikin binne baban abokinsa da ya mutu a jihar Osun.

"A shekarar da ta gabata an harbi abokinmu guda. Sannan kuma a watan Nuwamba, an kashe mini wani dan uwana, a lokacin da mu ke rikici da wata kungiyar irin ta mu.

KU KARANTA: Atiku ya fi Buhari sau dubu a wurina - in ji Obasanjo

"A karshen rikicin na kashe mutane biyu na kwace kayansu, daya daga cikinsu dan jihar Binuwai ne.

"A lokacin da 'yan sanda su ka kamani, an kai ni kotu amma an sake ni a watan Maris din da ya gabata. Tun lokacin dana dawo daga gidan yari, na kan je asibiti duba mahaifiyata wacce ta ke kwance ba lafiya. Ina ba wa iyalan mutanen da na kashe hakuri akan abinda ya faru, sannan ina rokon su da su yafe mini."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel