An zarce da Babban Lauya Ubani asibiti bayan ya sume a EFCC

An zarce da Babban Lauya Ubani asibiti bayan ya sume a EFCC

Mun samu labari cewa tsohon mataimakin shugaban Alkalan Najeriya na kungiyar NBA, Monday Ubani ya yanki jiki ya sare a yayin da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ke tsare da shi.

Monday Ubani ya zare jiki ne a cikin dakin da hukumar ta EFCC su ka tsare sa. Wannan ya sa aka ruga da shi zuwa wani asibiti a cikin Garin Abuja. Rahotanni sun nuna wannan abu ya faru ne a Ranar Talata 2 ga Watan Afrilu.

Tun a cikin Watan Maris ne Ubani da Christopher Enai, su ka shiga hannun EFCC inda ake neman su fito da tsohuwar shugabar hukumar NSITF watau Ngozi Olejeme wanda ake zargi da laifin satar kudin da ya haura Naira Biliyan 6.

KU KARANTA: An sace wani babban Jami'in Gwamnatin Tarayya a hanyar Abuja

Wani daga cikin Iyalin wannan Lauya ya bayyana cewa Monday Ubani ya kusa mutuwa ne a hannun EFCC a dalilin sikewa da yayi saboda rashin samun ruwa da kuma hawan-jini. Iyalin wannan Lauya sun koka da lamarin.

Wani daga cikin dangin wannan Lauya wanda ba zai so a fadi sunan sa ba, ya bayyana cewa Jami’an EFCC su na cigaba da tsare Ubani duk da cewa tuni babban kotun tarayya ta bada umarnin cewa a sake sa cikin gaggawa.

Kamar yadda mu ka ji, Lauya Monday Ubani ya kusa mutuwa in ban da cewa an ruga da shi zuwa asibiti. Lauyan yana ta kokarin nunawa EFCC cewa bai san inda Olejeme ta shige ba, tun bayan da aka dira gidan ta kwanakin baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel