Shari’ar Dasuki: Tana kasa tana dabo, Alkali ya sake dage sauraron karar

Shari’ar Dasuki: Tana kasa tana dabo, Alkali ya sake dage sauraron karar

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Abuja a karkashin jagorancin mai sharia Hussein Baba Yusuf ta sanya ranar 29 ga watan Afrilu don fara sauraron karar da aka shigar da kanal Sambo Dasuki da Bashir Yuguda akan zargin satar naira biliyan 19.4.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sauran wadanda ake tuhumarsu tare da Dasuki da Yuguda sun hada da tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, dansa Sagir da kuma kamfaninsa Dalhatu Investment Limited.

KU KARANTA: Rugum babban motsi: Motar tirela tayi gaba da gaba da jirgin kasa a jahar Jigawa

Shari’ar Dasuki: Tana kasa tana dabo, Alkali ya sake dage sauraron karar
Shari’ar Dasuki
Asali: Depositphotos

Hukumar EFCC na tuhumar mutanen ne akan aikata laifuka 25, wanda hakan yasa Alkali Hussein ya dage sauraron karar bayan jin korafe korafen Alkalan wadanda ake kara, inda suka bayyana rashin jin dadinsu da halartar Dasuki zaman kotun.

Da fari dai lauyan EFCC, Oluwaleke Atolagbe ya bayyana cewa sun yi iya kokarinsu don ganin DSS dake rike da Dasuki ta kawoshi gaban kotu, amma DSS ta bayyana musu cewa Dasuki ne da kansa yaki amincewa ya halarci zaman kotun.

Shi kuwa lauyan Bafarawa, Lateef Fagbemi bayyana damuwarsa yayi a gaban kotu game da yadda shari’ar ke tafiyar hawainiya, inda yace a karshen makonnan shari’ar ke cika shekaru hudu cif cif ana ta fafatawa, don haka yace idan EFCC ba zata iya ba ta janye karar kowa ya huta.

Daga karshe bayan Alkali Husseiniya dage shari’ar, sai kuma ya umarci hukumar EFCC data tabbata ta tsohon mashawarcin shugaban kasa akan harkar tsari Kanal Sambo Dasuki ya gurfana a gabanta don cigaba da shari’ar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel