Hukuma ta bayyana yan sandan da suka kashe matashi a gida kallon kwallo

Hukuma ta bayyana yan sandan da suka kashe matashi a gida kallon kwallo

Hukumar yan sandan jihar Legas, ta saki sunaye da hotunan jami'anta da suke da hannu cikin kisan wani matashi mai suna, Kolade Johnson, wanda aka harbe ba gaira ba dalili a gidan kallon kwallo.

Kolade Johnson ya rasa rayuwarsa ne yayinda yan sandan sashen yaki da yan daba suka dira gidan kallon kwallo dake Onipetesi, titin Lagos-Abeokuta ranar Lahadin da ya gabata inda ake taka leda tsakanin Liverpool da Tottenham.

Wannan abu ya tayar da hakulan jama'a a fadin tarayya wanda ya sanya hukumar yan sandan lashi takobin hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Hukuma ta bayyana yan sandan da suka kashe matashi a gida kallon kwallo
Hukuma ta bayyana yan sandan da suka kashe matashi a gida kallon kwallo
Asali: Twitter

KU KARANTA: Na fi kowani Bahaushe suna a duniya - Adam Zango (Bidiyo)

Kwamishanan yan sandan jihar Legas, Zubairu Muazu ya kai gaisuwar ta'aziyya ga iyalan Kolade Johnson ranar Talata inda ya tabbatar musu da cewa za'a hukunta jami'an da suke aikata wannan kisa.

Ba da dadewa ba, sai hukumar ta saki hotuna da sunayen jami'an a shafin Tuwita inda tace:

"Jami'an da ake zargi da harbin Kolade Johnson sun shiga hannu kuma ana gudanar da bincike kansu. Kwamishanan ya bayyana sunayensu: Insp Ogunyemi Olalekan da Sgt Godwin Orji."

A bangare guda, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo, ya jaddada goyon bayan sa ga tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya na karfafa tattalin arzikin Kasa.

Sambo ya ya bayyana hakan ne yayin jagorantar wata majalisi a ka yi don tattauna batun alakar masana'antu da noma don cigabar Najeriya. wannan majalisi ya gudana ne a yayin taron kasuwan baje-koli na arba'in a Jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel