Kasar Japan ta tallafa ma Najeriya da N540,000,000 don gina Arewa maso gabas

Kasar Japan ta tallafa ma Najeriya da N540,000,000 don gina Arewa maso gabas

Gwamnatin kasar Japan dake yankin Asiya ta Duniya ta tallafa ma kasar Najeriya da kyautar kudi dala miliyan daya da dubu dari biyar ($1,500,000) don sake gina yankin Arewa maso gabas wanda ayyukan kungiyar ta’addanci na Boko Haram suka lalata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kasar Japan ta bayyana haka ne a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu inda tace za’a kashe wadannan kudade ne a karkashin tsarin cigaba na majalisar dinkin duniya, UNDP da a yanzu haka yake gudana a Najeriya.

KU KARANTA: Rugum babban motsi: Motar tirela tayi gaba da gaba da jirgin kasa a jahar Jigawa

Kasar Japan ta tallafa ma Najeriya da N540,000,000 don gina Arewa maso gabas
Buhari da shugaban kasar Japan
Asali: UGC

Jakadan kasar Japan a Najeriya, Shigeru Umetsu yace wadannan kudade zasu karkata ne wajen kulawa tare da taimaka ma mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a jahohin Borno, Adamawa da Yobe domin su farfado daga mummunan halin da yakin ye jefasu.

“Wadannan kudi wani bangare ne na ayyukan jin kai da gwamnatin kasar Japan ke gudanarwa a yankin Arewa maso gabas ta hanyar, wasu daga cikin ayyukanta na baya sun hada da gyaran gine gine guda 20, da kuma daukan yan gudun hijira 2000 aikin wucin gadi.

“Haka zalika mun baiwa manoma fiye da 4,000 tallafin kayan aiki, kamar yadda muka taimaka ma masu kananan sana’o’I 1000 da tallafin jari, duk don su fadada hanyoyin samun kudaden shiga don gudanar da uzurorinsu. Zuwa yanzu mun kashe dala miliyan 6.5 a kokarin farfado da Arew maso gabas.” Inji shi.

Ita ma wakiliyar UNDP a Najeriya, Khardiata Lo Ndiaye ta bayyana irin tasirin da ire iren kudaden tallafin nan suke dasu ga jama’an yankin Arewa maso gabas, inda tace a yanzu haka tallafin yasa yan gudun hijira da dama sun dogara da kawunansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel