Hukumar ICPC ta fara bibiyan yadda yan majalisu suka kashe kudaden ayyukan mazabu

Hukumar ICPC ta fara bibiyan yadda yan majalisu suka kashe kudaden ayyukan mazabu

Hukumar yaki da rashawa da dangoginta, ICPC, ta bayyana cewa ta kaddamar da bincike don bibiyan yadda yan majalisu da yan kwangilarsu suka kashe kudaden ayyukan mazabu da gwamnati take basu, tare da nufin kama duk wanda ta kama da handame kudin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar, Farfesa Bolaji Owasanoye ne ya bayyana haka a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu yayin kaddamar da kwamitin bin diddigin ayyukan mazabu da yan majalisu ke gudanarwa a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Mutuwa riga: Matashi ya nutse a cikin ruwa a jahar Kano

“Zamu tilasta ma duk dan kwangilar da muka kama da laifin cinye kudin kwangilar ayyukan mazabu sai sun kammala ayyukan, ko kuma su dawo da kudin da suka ci, zamu buga sunayensu a jaridu tare da gurfanar dasu gaban kotu” Inji shi.

Haka zalika Owosanoye yace sun hada kai da cibiyar masana gine gine ta kasa domin ta duba yanayin ayyukan mazabu da yan majalisu suka yi domin tabbatar da ko sun cancanci kudin da aka kashe wajen gudanar dasu.

Bugu da kari shugaban yace tuni sun ware wasu hukumomin da ma’aikatun gwambati da zasu bibiyi ayyukansu don tabbatar da sun rage yiwuwar aikata rashawa a wadannan ma’aikatu da hukumomi.

Wasu daga cikin wadannan hukumomi sun hada da hukumar ilimi ta bai daya, UBEC, hukumar inshoran lafiya, NHIS, asusun ilimin gaba da sakandari, TETfund da sauransu, a cewar Owasanoye.

Daga karshe shugaban na ICPC yace matukar suka samu nasara a wannan gagarumin aikin da suka sanya a gaba, tabbas dan Najeriya zai samu sauki, sakamakon hukumomin nan zasu gudanar da aikinsu yadda ya kamata, kuma hakan karuwar dan Najeriya ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel