Za a ja daga a APC bayan Ndume ya fara shirin takara da Ahmad Lawan

Za a ja daga a APC bayan Ndume ya fara shirin takara da Ahmad Lawan

Yayin da ake shirin zaben shugabannin majalisar tarayya wannan karo, mun samu labari daga Jaridar Vanguard cewa akwai kwantaciyyar rikici a cikin gidan jam’iyyar APC mai mulki a halin yanzu.

Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya nuna cewa zai yi watsi da maganar shugaban APC watau Adams Oshiomhole, ya nemi takarar shugaban majalisar a zaben da za ayi.

Ali Ndume ya nuna cewa sam bai damu da zakulo Ahmad Lawan da jam’iyyar APC tayi a matsayin wanda zai gaji Bukola Saraki a majalisar dattawa ba. Ndume ya cigaba da shirin sa na neman wannan kujera a majalisa.

KU KARANTA: An yi sa-in-sa da ‘Yan Majalisa a zaman kasafin kudi da Minista

Tuni babban Sanatan ya gabatar da manufofin sa har 9 wanda yace idan ya samu kujerar shugaban majaliar dattawa zai dabbaka su. Daga ciki akwai kokarin ragewa ofishin na shugaban majalisa karfi na babu gaira babu dalili.

Mohammed Ali Ndume yace majalisa za ta ci gashin kan-ta idan ya samu wannan mukami, amma yayi alkawarin yin aiki da shugaban kasa sau-da-kafa. Ndume ya bayyana wannan shirin na sa ne a jiya 3 ga Watan Afrilun nan na 2019.

Matsayar jam’iyyar APC shi ne babu wanda zai yi takara da Ahmad Lawan, wanda Ali Ndume yana ganin hakan ba daidai bane domin ya sabawa tsarin majalisa da dokar kasa don haka yake fito-na-fito da jam’iyyar a halin yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel