2019: Murde zaben Kano Jam’iyyar APC ta yi - Alwan Hassan

2019: Murde zaben Kano Jam’iyyar APC ta yi - Alwan Hassan

Mun samu labari cewa wani daga cikin ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC mai mulki ya bayyana cewa babu zaben kirkin da aka yi a jihar Kano. Alwan Hassan ya bayyana wannan ne a gaban gidan talabijin kwanan nan.

Alwan Hassan wanda yana cikin ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kano ya fito yayi jawabi, akasin abin da jam’iyyar da kuma gwamnatin Kano ta ke fada, inda yace Gwamna Abdullahi Ganduje ya murde zaben da aka yi a 2019.

Mallam Hassan yayi wannan jawabi ne a lokacin da aka gayyace sa yayi bayani a shirin nan na Sunrise Daily. Hassan yace an kashe mutane yayin da aka raunata wasu Bayin Allah a lokacin da aka yi zaben cike-gibi a jihar.

Wannan Bawan Allah ya ajiye siyasa a gefe guda inda ya fede biri har wutsiya yana mai cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya fito ido rufe da niyyar komawa kan kujerar sa ko ta wani hali don haka zaben ya kare da rikici.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi magana a kan zaben Jihar Kano

Duk da cewa Hassan yana cikin manyan Magoya bayan shugaba Buhari, ya nuna cewa abin da APC tayi a jihar Kano bai dace ba, ya kara da cewa hakan na iya jawo wani babban rikici ya barke a jihar Kano idan aka yi sake.

Malam Alwan Hassan ya kuma bayyana cewa idan aka sake wani zabe gobe a jihar Kano, jam’iyyar su ta APC tana iya shan kashi ganin irin bakin jinin da wannan danyen aiki da APC tayi ya jawowa Shugaba Buhari a cikin Kano.

Wannan jagora na APC ya kuma dai wanke Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo daga wannan murdiya da aka tafka a Kano inda yace sam babu sa hannun su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel