'Yan bindiga sun sace babban jami'in NIMET

'Yan bindiga sun sace babban jami'in NIMET

Rahotanni da muka samu daga Daily Trust ya nuna cewa 'yan bindiga sun sace shugaban sashin hulda da al'umma na Hukumar Hasashen Yanayi na Kasa (NIMET), Muntari Ibrahim da akafi sani da 'Muntari Kwai' a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Dan sa mai suna Ibrahim Muntari ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce 'yan bindigan sun sace shi a yau da rana a lokacin da ya ke daawowa daga Abuja tare da dan uwansa, Tasi'u Isah.

A cewarsa, masu garkuwa da mutanen sun taho da motocci biyu inda suka tare gabansa da mota guda kirar Peugeot 408 yayin da wata motar na biyu ta tare bayansu.

DUBA WANNAN: Namadi Sambo ya goyi bayan Buhari a kan wasu muhimman tsare-tsarensa

'Yan bindiga sun sace babban jami'in NIMET
'Yan bindiga sun sace babban jami'in NIMET
Asali: Twitter

"Yan bindigan sun harba harsasai a iska kafin suka yi awon gaba da shi. Har yanzu ba su tuntube mu ba," inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa kawo yanzu, Muntari bai gama murmurewa daga raunin da ya yi ba sakamakon mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a 2018 da ya yi sanadiyar mutuwar direbansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel