Saboda rashin takardun sakandire: Kotu ta yi watsi da takarar Adeleke a PDP

Saboda rashin takardun sakandire: Kotu ta yi watsi da takarar Adeleke a PDP

- Kotu ta yi watsi da zaben Sanata Ademola Adeleke a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP, a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a Satumbar 2018

- Kotun ta ce Adeleke ya karya dokar sashe na 177 da ke a kundin dokar kasar da ya ce wajibi ne dan takarar gwamna ya mallaki matakin karatu har zuwa sakandire

- Sai dai lauyan Adeleke ya kalubalanci wannan hukunci da mai shari'a Musa ya yanke, yana mai cewa zai daukaka kara

Mai shari'a Oathman Musa a wata babbar kotu da ke da zama a karamar hukumar Bwari a Abuja a ranar Talata ta yi watsi da zaben Sanata Ademola Adeleke a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP, a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a watan Satumba 2018.

Adeleke, wanda ke wakiltar mazabar Osun ta Yamma a majalisar dattijai, shi ne ya lashe tikitin tsayawa takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar a watan Satumba.

Wasu kusoshin jam'iyyar APC guda biyu, Wahab Raheem da Adam Habeeb, a shekarar 2018, kwanaki kadan da zaben gwamnan jihar Osun, sun maka Adeleke gaban kotu, inda suka zarge shi da gaza mallakar sahihan takardun makarantar kammala sakandire, wanda a cewarsu bai cancanta ya tsaya takarar gwamnan jihar ba.

KARANTA WANNAN: Ba zamu iya gudanar da sabon zabe a Rivers ba - INEC ta ba jam'iyyu hakuri

Saboda rashin takardun sakandire: Kotu ta yi watsi da takarar Adeleke a PDP
Saboda rashin takardun sakandire: Kotu ta yi watsi da takarar Adeleke a PDP
Asali: Twitter

Da ya ke yanke hukunci a ranar Talata, mai shari'a Musa, ya soke zaben Adeleke a matsayin dan takarar PDP kasancewar ya karya dokar sashe na 177 da ke a cikin kundin dokar kasar na 1999 da aka yiwa kwaskwarima. Sashen ya ce wajibi ne dan takarar kujerar gwamna ya mallaki matakin karatu har zuwa sakandire.

A cewar mai shari'a Musa, a yayin da kotun ta tattara bayanai kan cewa Adeleke ya shiga makarantar sakandire a shekarar 1976, babu wani bayani da ya nunacewa ya kammala karatun kasancewar babu sunansa a cikin kundin daliban makarantar tun daga 1980.

Mai shari'a Musa ya kara da cewa takardar kammala makarantar da ke cikin kundinsa na CF001 wanda ya gabatarwa INEC na jabu ne, saboda an samu bayanai da suka banbanta kamar yadda shugaban makarantar Ede Muslim, Ede, jihar Osun ya gabatar.

A wani labarin makamancin wannan, lauyan Adeleke, Nathaniel Oke SAN ya kalubalanci wannan hukunci da mai shari'a Musa ya yanke, yana mai cewa mai shari'ar ya fita daga hurumi ta yadda har ya samo wasu hujjoji marasa tushe da ya yanke hukuncin da babu adalci a ciki.

Ya jaddada cewa kotun ta yi biris a lokacin da aka gabatar mata da takardun WAEC na shaidar cewa Adeleke ya yi karatu har zuwa makarantar sakandire.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel