Garkuwa da mutane: Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurnin sintiri kan hanyar Abuja

Garkuwa da mutane: Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurnin sintiri kan hanyar Abuja

Sakamakon hare-hare da garkuwa da mutanen da ya addabi babban hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Birnin gwari, majalisar tsaron jihar Kaduna ta yanke shawaran karfafa sintiri a hanyoyin domin rage hare-haren.

Mun kawo muku rahotannin yadda masu garkuwa da mutane suka dawo hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma hanyar birnin gwari. Tsakanin ranar Lahadi da Litinin kadai, an yi garkuwa da akalla mutane 42.

Duk da cewa hukumar yan sanda ta karyata yawan wadanda aka sace, kakakin hukumar ta jihar, DSP Sabo Aliyu, ya tabbatar da cewa an yi awon gaba da wasu mutane a mota kirar Hilux.

Sakamakon haka, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i wanda yake kasar Senegal ya tattauna da majalisar tsaron ta wayar tarho kuma sun yi ittifakin daukan mataki kan al'amarin da wuri.

KU KARANTA: Saudiyya ta yankewa yan Najeriya 8 haddin kisa, wasu 20 na kan layi

Game da cewar mai magana da gwamnan, Samuel Aruwan, bayan sintiri da za'a kara zurfafawa, za'a kara karfin tsaro a dukkan sassan jihar.

Gwamnatin ta tabbatarwa mazauna jihar su cigaba da baiwa jami'an tsaron goyon baya wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.

An bayar da lambobin da za'a iya kira a koda yaushe, ga lambobin: 09034000060 da 08170189999.

Mun kawo muku da safe cewa gungun miyagu yan bindiga sun kai farmaki akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, inda suka tare motoci da dama tare da yin awon gaba da matafiya da dama zuwa cikin dazuka da nufin yin garkuwa dasu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi sanadiyyar aukuwar hadarurruka da dama akan babbar hanyar yayin da suka tilasta ma motoci tsayawa duk kuwa da mugun gudun da wasu motocin ke yi, sa’annan sun kwace kudade, wayoyi da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel