Zababen gwamnan jihar Zamfara ya shigar da karar INEC a kan takardan cin zabe

Zababen gwamnan jihar Zamfara ya shigar da karar INEC a kan takardan cin zabe

A kalla jam'iyyun siyasa 20 ne daga jihar Zamfara su kayi karar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC a kan rashin bawa zababen gwamnan jihar Zamfara da 'yan majalisun dokokin jihar takardun shaidan cin zabe.

Ebenezer Adabaki ne ya shigar da karar a ranar Talata a babban kotu da ke zamanta a Abuja a madadin masu shigar da karar.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Shugaban kungiyar jam'iyyun siyasa na Zamfara, Zayyanu Haske, Zababen gwamnan jihar, Mukhtar Idris, mataimakinsa, da zababun 'yan majalisun dokoki 24.

DUBA WANNAN: Tinubu ya fadawa mambobin APC masu adawa da zabin Lawan abinda yafi dacewa suyi

Kin bashi takardan shaidan cin zabe: Zababen gwamnan Zamfara ya maka INEC a kotu
Kin bashi takardan shaidan cin zabe: Zababen gwamnan Zamfara ya maka INEC a kotu
Asali: Facebook

Masu shigar da karar suna son kotu ta tabbatar idan sashi na 133(1) da 155 na dokar zabe ya bawa INEC ikon hana ko rashin bayar da kula ga batun bawa 'yan takarar da suka ci lashe takardun shedan cin zaben.

"Shin ko matakin da INEC ta dauka na dakatar da bayar da takardan shaidan cin zabe ga 'yan takarar da suka lashe zaben gwamna da 'yan majalisun tarayya na jihar Zamfara bai sabawa doka ba ko kuma sakacin aiki."

Wadanda suka shigar da karar sun bukaci kotu ta tursasawa INEC bawa zababen gwamnan da mataimakinsa da sauran mambobin majalisar dokokin jihar ba tare da bata lokaci ba.

Sai dai a halin yanzu ba tsayar da ranar da za a fara sauraron shari'ar.

DUBA WANNAN: Tinubu ya fadawa mambobin APC masu adawa da zabin Lawan abinda yafi dacewa suyi

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel