Kalaman Sanata Melaye sun zama gaskiya bayan an fara shirin tsige CJ a Kogi

Kalaman Sanata Melaye sun zama gaskiya bayan an fara shirin tsige CJ a Kogi

A jiya ne Litinin ne Sanata Dino Melaye mai wakiltar yankin Kogi ta yamma a majalisar dattawan Najeriya yace ana shirin tsige Alkalin Alkalan jihar Kogi watau Alkali mai shari’a Nasiru Ajanah.

Dino Melaye ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kogi ta kudiri niyyar yin waje da babban Alkalin jihar a cikin farkon makon nan. Sanata Melaye yayi wannan magana ne a shafin sa na sada zumunta na yanar gizo na Tuwita.

Melaye ya bayyana wannan ne a Ranar 4 ga Watan Afrilun 2019, yana mai takaicin halin da jihar ta shiga. Sanatan yace a jiya ne gwanatin jihar Kogi ta ba kakakin majalisar dokoki umarnin ya sauke CJ Nasiru Ajanah yau dinnan.

Fitaccen ‘dan majalisar ya nuna cewa za su tsaya tsayin-daka wajen ganin cewa gwamnatin Yahaya Bello ba tayi nasarar sauke babban Alkalin jihar ba. Tuni dai wasu su ka fara zanga-zanga domin nuna rashin amincewar su.

KU KARANTA: Majalisa ta bayyana ranar da ake sa rai kasafin kudin 2019 zai soma aiki

Sai dai a yau kwatsam majalisar jihar ta Kogi ta wayi gari da batun sauke Mai shari’a Nasiru Ajanah daga kan kujerar Alkalin Alkalai inda ta zarge sa da aikata laifuffuka da su ka sabawa ka’idar aikin shari’a a Najeriya.

Marasa rinjaye a majalisar sun yi yunkurin dakatar da wannan yunkuri a zaman da aka yi sai kakakin majalisar yayi watsi da wannan roko. Kafin yau dai dama Emmanuel Waniko ya zargi gwamnan jihar da kitsa wannan shiri.

Majalisar ta kuma nemi gwamnatin jihar Kogi ta cigaba da biyan ma’aikatan shari’a albashin su. Kwanaki kun ji cewa rashin albashin yayi sanadiyyar mutuwar wani Ma’aikaci a Jihar Kogi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel