Namadi Sambo ya goyi bayan Buhari kan tsare-tsaren sa na tattalin arziki

Namadi Sambo ya goyi bayan Buhari kan tsare-tsaren sa na tattalin arziki

A ranar Talata ne tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo, ya jaddada goyon bayan sa ga tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya na karfafa tattalin arzikin Kasa.

Sambo ya ya bayyana hakan ne yayin jagorantar wata majalisi a ka yi don tattauna batun alakar masana'antu da noma don cigabar Najeriya. wannan majalisi ya gudana ne a yayin taron kasuwan baje-koli na arba'in a Jihar Kaduna.

Sambo ya kuma yabawa Gwamnatin Najeriya game da kokarin ta na bunkasa harkar kasuwanci, ya kuma sakankance wadannan tsare-tsaren za su karfafa tattalin arziki ga barin dogaro a kan man fetur kadai.

A cewar sa, dokokin Gwamnatin musamman na shigowan kayaki musamman wadanda za a iya samar da su a cikin gida Najeria, zai habaka tattalin arzikin kuma ya ciyar da kasa gaba.

DUBA WANNAN: Tinubu ya fadawa mambobin APC masu adawa da zabin Lawan abinda yafi dacewa suyi

Namadi Sambo ya goyi bayan tsare-tsaren tattalin arzikin Buhari
Namadi Sambo ya goyi bayan tsare-tsaren tattalin arzikin Buhari
Asali: Twitter

Sambo bai gushe ba ya na bayyana bukatuwar a rinka saye da amfani da kayakin da aka sana'anta a gida don ta haka ne za a bunkasa tattalin arzkin a saukake kuma cikin sauri.

Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Nasiru El-Rufa'i a game da kasuwanci, hako ma'adanai da kuma noma. Ya kuma yaba game da kokarin da Gwamnatin Jihar ke yi na ganin ta kammala aikin da ta dauko na bunkasa wuta lantarki.

Ita kuwa jagorar wannan majalisi, ta Muheebah Dankaka, ta bayyana cewar taken kasuwan baje-kolin na bana, an fitar da shi don ingiza muhawara a kan kokarin Gwamnati wurin bunkasa tattalin arziki ta hanyar noma da masana'antu.

Shi kuwa bako mai jawabi, Farfesa Nazifi Abdullahi Drama wanda masani ne kan tattalin arziki a Jami'ar Abuja, ya yi kira da a kara dankon zumunci tsakanin sassa da-ban da-ban don bunkasa tattalin arziki kamar yadda Kamfanin Dillacin Labarai, NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel