An samu takaddama da Okechukwu Enelamah a Majalisa a game da kasafin kudin 2019

An samu takaddama da Okechukwu Enelamah a Majalisa a game da kasafin kudin 2019

Labari ya zo mana cewa an nemi ayi hanayaniya yayin da ake wani zama na musamman da ya shafi aikin kasafin kudin wannan shekarar. An samu surutu ne tsakanin Sanatoci da Okechukwu Enelamah.

‘Yan majalisa sun kira Ministan harkokin kasuwanci na Najeriya, Dr. Okechukwu Enelamah, ya kare kason da aka warewa ma’aikatarsa a cikin kundin kasafin kudin bana. A wajen wannan zama ne magana ta kai har ta kawo a Majalisar.

An fara samun matsala ne bayan da aka gano cewa Ministan ya warewa wani kamfani kudi har Naira Biliyan 42. Wannan ya sa kwamitin da ke lura da harkar kasuwanci a majalisar dattawa su ka nemi karin bayani daga bakin Ministan.

Wannan kudi da aka warewa wani kamfani mai zaman kan-sa, ya sha ban-ban da kason kudin da ake ba ma’aikatar a kowace shekara. Ministan yayi kokarin nunawa Sanatoci cewa gwamnatin tarayya na da hannu a harkar wannan kamfani.

KU KARANTA: An gargadi APC ta guji kakabawa Majalisa shugabanni a 2019

An samu takaddama da Okechukwu Enelamah a Majalisa a game da kasafin kudin 2019
Ana zargin Enelamah ya cusawa wani kamfani kudi a kasafin kudin bana
Asali: Depositphotos

Ashe dai tuni wani Sanatan Jigawa watau Sabo Mohammed ya gama binciken sa game da wannan kamfani inda ya fadawa Ministan cewa abin da ya fada ba gaskiya bane, domin kuwa wasu ‘yan kasuwa ne ainihin masu wannan kamfani.

Bayan nan kuma Sanata Sabo Mohammed ya fayyacewa Ministan cewa ya gano cewa a 2018 aka bude wannan kamfani kuma bai da wata alaka da aikin samar da hanyoyi ko bunkasa masana’antu kamar yadda Ministan yayi masu ikirari.

Leadership ta rahoto mana cewa a dalilin haka ne kwamitin tayi fatali da kudin da aka warewa wannan ma’aikata a kasafin kudin shekarar nan. Dazu ne dai mu ka ji cewa an bayyana ranar da ake sa rai za a gama aikin kasafin kudin 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel