Buhari da Obasanjo sun hadu karo na farko bayan zabe

Buhari da Obasanjo sun hadu karo na farko bayan zabe

Shugaban kasa muhammdu Buhari da tsohon Shugaban kasa olusegun Obasanjo sun hadu a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu.

Sun hadu ne a wajen bikin rantsar da Shugaban kasa macky sall na Senegal a Dakar.

A daya daga cikin hotunan an gano shugaba Buhari tare da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo; shugaban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina; shugaba Sahara Power Group Mista Kola Adesina, da shugaban bankin UBA, Tony Elumelu.

Koda dai Obasanjo ya kasance babban dan adawar gwamnatin Buhari, an gano su suna dariya da raha da juna kamar babu wani abu a tsakaninsu na kushe.

Buhari da Obasanjo sun hadu karo na farko bayan zabe
Buhari da Obasanjo sun hadu karo na farko bayan zabe
Asali: Facebook

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana tsohon mataimakin sa, Atiku Abubakar a matsayin mutumin da ya fi shugaba Buhari iya siyasa, wayewa da kuma koshin lafiya.

Obasanjo ya ce, duk da cewa kowanne mutum tara ya ke bai cika goma ba, amma ya na da tabbacin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya fi shugaban kasa Muhammadu Buhari sau dubu.

A cewar tsohon shugaban kasar, Atiku wanda ya yi mishi mataimaki a lokacin da ya yi mulki, ya fi shugaba Buhari, ta fannin sannin kan siyasa, fannin tattalin arziki da kuma wayewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel