Saudiyya ta yankewa yan Najeriya 8 haddin kisa, wasu 20 na kan layi

Saudiyya ta yankewa yan Najeriya 8 haddin kisa, wasu 20 na kan layi

Akalla yan Najeriya takwas sun fuskanci fushin shari'a a kasar Saudiyya inda aka yanke musu haddin kisa sakamakon ta'amui da muggan kwayoyi, shugaban hukumar jin dadin yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri, ta tabbatar.

Dabiri ta bayyanawa manema labaran fadar shugaban kasa yayinda take tsokaci kan kisan wata mata yar Najeriya a Saudiyya sakamakon laifin hulda da kwayoyi.

Dabiri, yayinda take nuna bacin ranta kan kisan yan Najeriya, ta ce akwai wasu guda ashirin yanzu dake kan layi za'a yanke musu haddi.

Yayinda take kira ga hukumomin kasar Saudiyya ta baiwa yan Najeriya daman samun hukunci mai sauki, ta bayyana cewa kamfanonin jirgin Misra da Habasha na da hannu cikin masu daukan wadannan kwayoyi.

Ta yi kira ga yan Najeriya su kasance abin alfahari ga kasa, ba kaman wadanda aka kama jiya Litinin ba a kasar Dubai da suka zama abin kunya ga kasar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya halarci taron rantsar da shugaban kasar Senegal (Hotuna)

Mun kawo muku rahoton cewa jaridar kasar Saudiyya ya bayyana cewa an kashe wata mata 'yar Najeriya da ta ke zaune a kasar Saudiyya bayan kama ta da hukumar kasar ta yi tana safarar miyagun kwayoyi.

An kashe matar ne, ita da wasu maza guda biyu 'yan asalin kasar Pakistan da kuma wani namiji guda daya dan kasar Yemen. An yanke musu hukuncin kisan ne a birnin Makka, birni mafi tsarki a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel