Hukumar NIS tayi karin girma ga manyan jami'ai 14

Hukumar NIS tayi karin girma ga manyan jami'ai 14

Shugaban hukumar shige da fice ta kasa (NIS), Muhammad Babandede, ya yiwa wasu manyan jami'ai 14 da aka kara wa girma kwalliya da lambobin samun karin matsayi.

A wurin bikin kara wa manyan jami'an girma, Babandede ya bayyana cewar suna daga cikin jami'an hukumar 21 da suka samu karin matsayi.

Ya ce an kara wa manyan jami'an girma zuwa mukamin mataimakin shugaba na kasa (ACG), ya kara da cewa 9 daga cikinsu maza ne da mata 5.

"7 daga cikinsu sun yi ritaya kafin a kara masu mukami bayan sun rubuta jarrabawar neman karin matsayi.

Hukumar NIS tayi karin girma ga manyan jami'ai 14
Mohammed Babandede
Asali: Depositphotos

"Babu wata hukuma a Najeriya da ke bawa maza da mata dama bai daya kamar hukumar NIS.

"Ina mai kira ga sabbin ACGs da su zama masu hali me kyau da na kasa zasu kwaikwaya. Ba iya samun mukamin ba ne, akwai bukatar ku kasance masu hali me kyau a ciki da wajen wurin aiki.

"Krin girma girma yana nufin karin dage wa da nuna kishi a kan aiki.

DUBA WANNAN: INEC ta sake dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Ribas

"Aikin ku ba na siyasa ba ne, a saboda haka dole ku dage, ku nuna kishi da kwazo kafin samun karin girma zuwa mukami na gaba," a cewar Babandede.

A jawabin Aminu Mohammed, daya daga cikin jami'an da suka karin matsayin, ya nuna jin dadinsa da jazircewar Babandede a kan inganta aiyukan hukumar NIS.

"Amadadin ragowar abokaina da muka samu karin girma tare, ina bawa shugabanmu tabbacin cewar ba zamu ba ka kunya ba," a cewar Aminu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel