Yadda ta kasance bayan wata budurwata ta koma musulunci, ta canja suna

Yadda ta kasance bayan wata budurwata ta koma musulunci, ta canja suna

Wani dan Najeriya ya bayar da labarin yadda rahotanni suka bayyana cewa wata mata a Abuja ta karbi musulunci har ta canja sunanta zuwa na musulmi. Al'umma da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu a kan labarin.

Wani mutum mai suna Abbakar Sadeeq a Twitter ya bayyana murnarsa a kan yadda wata budurwa mai suna Blessing wadda Kirista ce a baya ta karbi addinin musulunci.

Ya bayyana matukar farin ciki a kan lamarin inda ya yi addu'a Allah ya kara mata imani a cikin addinin na musulunci. Abbakar ya kuma ce Blessing ta canja sunanta zuwa Zainab bayan da ta musulunta.

Baya ga haka, ya nuna hotunan budurwar da ke zaune a garin Abuja a shekarun baya kafin ta musulunta da kuma hoton ta bayan ta musulunta sanye da hijabi.

Ga hotunan a kasa:

"Allah Akbar ta karbi musulunci a jiya nan a Abuja. Ta canja sunanta daga Blessing zuwa Zainab. Allah ya kara mata imani..."

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu a kan labarin. Mafi yawancin su sun taya ta murna inda suka ce tafi kyau a yayin da ta sanya hijabi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel