INEC ta sake dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Ribas

INEC ta sake dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Ribas

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dakatar da ttara sakamakon zaben gwamnan jihar da ta fara a yau, Talata.

Kwamishiniyar INEC a jihar Ribas, Obo Effanga, ne ya sanar da hakan a cibiyar tattara sakamako da ke garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

A cewar ta, hukumar zabe zata cigaba da tattara sakamakon da misalin karfe 10 na safiyar ranar Laraba.

Ta bayar da sanarwar ne bayan kammala karbar sakamakon zaben gwamnan da aka tattaro daga kananan hukumomi 15 na jihar.

Rahotanni sun bayyana cewar jam'iyyar PDP ce a gaba daga sakamakon kananan hukumomin da INEC ta karba a cibiyar tattara sakamako ta jiha.

Kotu ta sake dakatar da tattara sakamakon zaben jihar Ribas
Cibiyar tattara sakamako ta INEC
Asali: Original

Jam'iyyar APC ba ta da dan takarar gwamna a jihar Ribas. Hakan ya biyo bayan gaza gudanar da zaben fidda 'yan takara da jam'iyyar tayi a kan lokaci.

Hakan ne yasa jagoran jam'iyyar APC a yankin kudu maso kudu kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewar magoya bayan APC su zabi jam'iyyar AAC a zaben gwamnan jihar.

DUBA WANNAN: Fyade a sansani 'yan gudun hijira: Kotun sojoji ta kori wani soja daga aiki

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ne ke yin takarar gwamna a karo na biyu a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

INEC ta dakatar da dukkan wasu harkokin da suka shafi zaben gwamna a jihar Ribas bayan an samu barkewar rikici a sassan jihar da dama yayin gudanar da zaben gwamna da mambobin majalisar dokoki na ranar 16 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel