Yanzu Yanzu: Na hannun daman Amosun ya sauya sheka daga APM, ya koma APC

Yanzu Yanzu: Na hannun daman Amosun ya sauya sheka daga APM, ya koma APC

- Na hannun damar gwamna Ibikunle Amosun, Mista Adeyinka Mafe ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM)

- Mafe ya sanar da komawrsa zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC)

Mista Adeyinka Mafe, Shugaban masu rinjaye a majalisan dokokin jihar Ogun kuma na hannun damar gwamna Ibikunle Amosun, a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM).

Mafe, dan majalisa mai wakiltan Sagamu 1 a majalisar dokokin jihar, ya bayyana a wasikar janyewarsa wanda Mista Suraj Adekumbi, kakakin majalisar ya karanta cewa, ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Yanzu Yanzu: Na hannun daman Amosun ya sauya sheka daga APM, ya koma APC

Yanzu Yanzu: Na hannun daman Amosun ya sauya sheka daga APM, ya koma APC
Source: Depositphotos

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta rahoto cewa Mafe tare da wasu mambobi uku a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2018 sun bar APC zuwa APM.

Yan majalisan sun bayyana janyewarsu a wasikun daban-daban da suka aika majalisar wanda kakakin majalisan ya karanta a zauren majalisa.

KU KARANTA KUMA: Najeriya na daya daga cikin kasashen da ba a bin su bashi sosai a duniya - Osinbajo

Sauran yan majalisan guda ukun sun hada da bulaliyar majalisa, Idowu Olowofuja mai wakiltan kudancin Abeokuta na II, Ganiyu Oyedeji (Ifo II) da kuma Tunde Sanusi (Obafemi Owode).

Kamfanin Dillancin Labarai ta rahoto cewa tunda Mafe ya sauya sheka daga jam’iyyar APM, ba a zabi sabon shugaban majalisa mafi rinjayi ba a halin da ake ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel