Fyade a sansani 'yan gudun hijira: Kotun sojoji ta kori wani soja daga aiki

Fyade a sansani 'yan gudun hijira: Kotun sojoji ta kori wani soja daga aiki

Wata kotun da'ar sojoji ta musamman da ke zamanta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ta kori wani soja daga aiki bayan samunsa da laifin aikata fyade ga wata budurwa mai shekaru 14 da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira (IDP).

Laftanal Martins Owerrem, shine sojan da aka kora daga aiki kamar yadda shugaban kotun, Manjo Janar Yakubu Auta, ya bayyana.

An gurfanar da Owerrem a gaban kotun bisa aikata laifin saba wa dokar aiki, cin mutunci da fyade.

Da yake yanke hukunci a yau, Talata, Auta ya ce, "bisa dogaro da hujjojin da aka gabatar, wannan kotu mai daraja ta gamsu cewar wanda ake tuhuma ya aikata fyade ga yarinyar.

"Wanda ake tuhumar da kansa ya amsa cewar ya mari yarinyar sannan ya ja ta a kasa tare da saka yatsansa a farjinta.

"Wannan kotu ta same ka da aikata laifuka 2 daga cikin uku da ake tuhumarka da aikata wa."

Fyade a sansani 'yan gudun hijira: Kotun sojoji ta kori wani soja daga aiki

Kotun sojoji ta kori wani soja daga aiki
Source: Twitter

A daya daga cikin laifukan, kotun ta kori sojan daga aiki. Kotun ta wanke sojan daga aikata laifi na biyu da ake tuhumarsa da shi. Kazalika kotun ta yanke wa sojan hukuncin rage masa mukami a laifi na uku da ake tuhumarsa da aikata wa.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda ta karayata labarin sace mutane 30 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Auta ya rufe sauraron karar bayan kammala karanta hukuncin da aka yanke wa Owerrem.

Owerrem ya aikata laifin fyade, a shekarar 2018, ga wata yarinya mai shekaru 14 a sansanin 'yan gudun hijira lokacin da ya ke jagorantar wata bataliyar sojoji da sansaninta ke kusa da Bakassi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel