Wata tsohuwa yar shekara 77 ta kammala karatun digiri a UNILAG

Wata tsohuwa yar shekara 77 ta kammala karatun digiri a UNILAG

- Tsohuwa yar shekara 77, ta kammala karatun digiri a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu daga jami’ar Legas wato UNILAG

- Matar wacce ta ki bayyana sunanta ta karanci fannin bayar da shawarwari wato “Guidance and Counselling”

- Tana daga cikin dalibai 12,843 wadanda suka kammala karatun digiri daga jami’ar a bikin kammala digiri karo na 50

Wata tsohuwa yar shekara 77, ta kammala karatun digiri a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu daga jami’ar Legas (UNILAG) tare da abokan karatunta.

Ta karanci fannin bayar da shawarwari wato “Guidance and Counselling”.

Ta kasance daga cikin dalibai 12,843 wadanda suka kammala karatun digiri daga jami’ar a bikin kammala digiri karo na 50.

Wata tsohuwa yar shekara 77 ta kammala karatun digiri a UNILAG
Wata tsohuwa yar shekara 77 ta kammala karatun digiri a UNILAG
Asali: UGC

An kira ta zuwa dandamalin dakin taron don karramawa tare da gaisawa da kuma hoto da shugaban jami’ar, Dr. Wale Babalakin, mataimakin shugaban jami’ar, farfesa Oluwatoyin Ogindipe da sauran manyan jami’i da ke a dakin taron.

Tsohuwar wace ta kasance ma’aikaciya mai ritaya, ta zo makarantan ne don karin ilimi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin Kogi ta dakatar da Shugaban alkalan jihar

Duk da haka, ta ki bayyana sunan ta sannan ta ki yin wani karin bayani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel