Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin Kogi ta dakatar da Shugaban alkalan jihar

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin Kogi ta dakatar da Shugaban alkalan jihar

Majalisar dokokin jihar Kogi a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu ta dakatar da shugaban alkalan jihar, Justis Nasir Ajana.

Hakan na zuwa ne duk da zanga-zangar da kungiyoyin jihar suka yi don gargadi akan lamarin.

Kafin wannan yunkurin, Legit.ng ta tuna cewa sanata mai wakiltan Kogi ta yamma, Dino Melaye, ya bayar da tsegumi kan yunkurin dakatar da Justis Ajana daga kan kujerarsa.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Sanatan Kogin ya sanar da cewa an kammala shiri tsaf domin tsige babban alkalin alkalan jihar.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta raht cewa rundunar 'yan sanda reshen jihar Kaduna ta ce babu gaskiya a cikin wani labari dake kewaya a dandalin sada zumunta da wasu kafafen yada labarai a kan cewar an sace wasu mutane 30 a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

KU KARANTA KUMA: Wata tsohuwa yar shekara 77 ta kammala karatun digiri a UNILAG

DSP Yakubu Sabo, kakakin rundunar a jihar Kaduna, ne ya karyata labarin sace mutanen a wata sanarwa da ya fitar yau, Talata, a Kaduna.

Sabo ya bayyana cewar hanakalin rundunar 'yan sanda ya kai kan labarin bogin da ake yada wa a dandalin sada zumunta a kan cewar an sace wasu mutane su 30 a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 1 ga watan Afrilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel