Jam'iyyar ADC ta shawarci Buhari akan neman yafiyar Alkalin Alkalai, Onnoghen

Jam'iyyar ADC ta shawarci Buhari akan neman yafiyar Alkalin Alkalai, Onnoghen

Rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyar ADC, African Democratic Congress, ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta neman gafarar Alkalin Alkalai na kasa da ya dakatar, Mai shari'a Walter Onnoghen.

Jam'iyyar ta kuma bayyana cewa, za ta ci gaba da goyon bayana dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a yayin da ya ke ci gaba da fafutikar kwato hakkin sa na nasarar zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Jam'iyyar ADC ta shawarci Buhari akan neman yafiyar Alkalin Alkalai, Onnoghen
Jam'iyyar ADC ta shawarci Buhari akan neman yafiyar Alkalin Alkalai, Onnoghen
Asali: UGC

Kwamitin shugabannin jam'iyyar ADC, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya gabatar a ranar Talata bayan taron da ya gudanar a babban birnin kasar nan na tarayya. Jam'iyyar ADC ta kushe yadda babban zaben kasa ya gudana a bana.

Jam'iyyar ADC ta yi ikirarin cewa, hukumomin kasar nan da suka hadar da EFCC, ICPC, NCC, da kuma uwa uba hukumar INEC, sun taka muhimmiyar rawar gani wajen danne hakkin mambobin ta da su ka fafata wajen neman kujerun siyasa yayin zaben bana.

Sanarwar da manema labarai su ka gabatar ta gudana ne da sa hannun kakakin jam'iyyar nakasa, Yemi Kolapo, Sakataren ta Alhaji Said Abdullahi da kuma shugaban ta na kasa baki daya, Ralph Nwosu.

KARANTA KUMA: Asibitin Villa na 'yan cikin fadar shugaban kasa ne kadai - Buhari

A yayin kiran shugaban kasa Buhari domin ya gaggauta neman gafarar Alkalin Alkalai na kasa da ya dakatar tare da mai she masa da mukamin sa, jam'iyyar ADC ta ce dimokuradiyya ba za ta tabbata ba a Najeriya matukar gwamnati za ta ci gaba da dakile 'yancin al'umma.

Domin ci gaba da kwararar romon dimokuradiyya, jam'iyyar ADC ta yi karin haske kan yiwa dokoki da kuma kundin tsarin mulkin kasa da'a tare da dawowa daga rakiyar zamani na alfarma musamman a tsakankanin 'yan siyasa da masu rike da madafan iko wajen yiwa kowa adalci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel