Asibitin Villa na 'yan cikin fadar shugaban kasa ne kadai - Buhari

Asibitin Villa na 'yan cikin fadar shugaban kasa ne kadai - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya umarci cibiyar lafiya da ke cikin fadar shugaban kasa SHMC, State House Medical Centre, da ta dawo bisa turba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta daidai da tsari na manufar da aka assasa ta.

Mataimakin shugaban cibiyar sadarwa na fadar shugaban kasa, Attah Esa, shi ne ya yi wannan karin haske da sanadin Sakataren dindindin na fadar shugaban kasa, Jalal Arabi, da ya bayyana a ranar Litinin.

Asibitin Villa na 'yan cikin fadar shugaban kasa ne kadai - Buhari
Asibitin Villa na 'yan cikin fadar shugaban kasa ne kadai - Buhari
Asali: UGC

Mista Arabi ya bayyana hakan a yayin kafa hujjoji da amsa tambayoyin kwamitin majalisar dattawa akan harkokin tabbatar da da'a a ma'aikatun gwamnatin tarayya da suka shafi kasafin kudin kasa na bana.

Cikin dalilai da babban Sakataren ya bayyana, shugaban kasa Buhari ya nemi a haramtawa sauran gama garin Mutane cin moriyar cibiyar Lafiya ta fadar Villa domin saukake ma ta nauyin gudanarwa.

A yayin da gwamnati ke tanadin kasafin kudi ga cibiyar Lafiya da ke cikin fadar Villa domin kulawa da lafiyar shugaban kasa, mataimakin sa, iyalan su da kuma sauran masu ruwa da tsaki na fadar, ci gaba da bai wa sauran gama garin mutane dama ta neman lafiya a cibiyar zai haifar da nakasun inganci da kuma nakasun nagarta wajen tabbatar da manufar da aka kafa ta.

KARANTA KUMA: Ba mu da nufin sayar da man fetur sama da N145 - 'Yan kasuwa

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, shugaban kasa Buhari ya ce ba zai yiwu sauran gama garin Mutane su ci gaba da cin moriyar cibiyar Lafiya ta fadar Villa ba a yayin da karfin ikon ta ya takaita kadai kan al'ummar cikin fadar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel