Ba mu da nufin sayar da man fetur sama da N145 - 'Yan kasuwa

Ba mu da nufin sayar da man fetur sama da N145 - 'Yan kasuwa

Kungiyar 'yan kasuwa da dillalan man fetur mai zaman kanta IPMAN, Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria, a reshen ta na jihar Kano ta bayyana matsaya dangane da yiwuwar kara farashin man fetur doriya akan N145 da ya ke kai a yanzu.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, kungiyar IPMAN reshen jihar Kano ta ce ba ta da wani nufi ko kuma kudiri na kara farashin man fetur a kasar nan doriya akan N145 farashin lita guda ta man fetur da ya ke kai a halin yanzu.

Ba mu da nufin sayar da man fetur sama da N145 - 'Yan kasuwa
Ba mu da nufin sayar da man fetur sama da N145 - 'Yan kasuwa
Asali: UGC

Kungiyar ta yi kira na neman al'ummar Najeriya da su nuna halin ko in kula tare da watsi da barazanar jagoran kungiyar na kasa baki daya, Shina Amoo.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Alhaji Bashir Dan Malam, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata cikin birnin Kanon Dabo.

Ya yi martani kan furucin shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Mista Shina Amoo, wanda ya yi bambami na barazana ta cewar akwai yiwuwar za a fara sayar da man fetur akan farashi sama da N145 muddin dillalai su ka ci gaba da bayar sari akan N136.5 zuwa 137 na kowace lita guda.

KARANTA KUMA: Masu garkuwa da Mutane sun yashe Mutane 8 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Dan Malam ya ce kungiyar za ta ci gaba da sayar kowace lita guda ta man fetur akan N145 kamar yadda gwamnatin tarayya ta kayyade, kuma hukumar kula da ma'adanan man fetur ta kasa DPR, za ta tsaurara matakai wajen hukunta wadanda suka sabawa wannan doka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel