Rashin tsaro a Najeriya ya na kuntata min - Aisha Buhari

Rashin tsaro a Najeriya ya na kuntata min - Aisha Buhari

Aisha Buhari, uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta bayyana bakin cikin ta dangane da yadda tabarbarewar tsaro a Najeriya ke kuntata mata yayin da ta yi kira na neman dukkanin masu ruwa da tsaki su hada gwiwa wajen yakar miyagun ababe masu barazana da zaman lafiya.

Uwar gidan shugaban kasa yayin bayyana takaicin ta dangane da manyan kalubale da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu, ta yi kira na neman dukkanin masu ruwa da tsaki wajen hada gwiwa da hukumomin tsaro domin tsarkake kasar nan daga miyagun ababe masu kawo tagarda ta kwanciyar hankali.

Rashin tsaro a Najeriya ya na kuntata min - Aisha Buhari
Rashin tsaro a Najeriya ya na kuntata min - Aisha Buhari
Asali: Getty Images

Hajiya Aisha ta yi wannan kira a ranar Talata yayin bikin kaddamar da wani littafi da wasu marubuta uku suka wallafa kan rawar da dakarun soji ke takawa a Najeriya wajen bayar da kariya da kuma tsaro.

Kungiyar Matan Dakarun Soji da kuma na 'Yan sanda DEPOWA, Defence and Police Officers Wives Association, ita ce ta dauki nauyin wannan taro da aka gudanar a cikin garin Abuja kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Aisha ta yi kira na gargadin al'ummar Najeriya da su tashi su farga tare da sanya idanun lura wajen bayar da muhimman rahoto da za su taimakawa hukumomin tsaro wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan su yayin tukarar duk wasu ababe masu cin karo da zaman lafiya.

KARANTA KUMA: Ku lura da irin ababen da za ku rika shiga da su kasar Saudiya - Gwamnatin tarayya ta gargadi 'yan Najeriya

Ta yi kira ga 'yan uwanta Mata da suka kasance Iyaye akan su sanya idanun lura akan kai kawo da kuma shige da fice na 'ya'yayensu wajen ba su tarbiya nagartacciya da za ta zame masu tasiri na kyakkyawar makoma a kansu da kuma kasa baki daya.

Ta kuma yabawa kwazon gwamnatin shugaban kasa Buhari musamman yadda ta jajirce wajen samun nasarori yayin da ci gaba da yakar ta'addanci da ya zamto tamkar karfen kafa tare da hana ruwa guda a kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel