Ku lura da irin ababen da za ku rika shiga da su kasar Saudiya - Gwamnatin tarayya ta gargadi 'yan Najeriya

Ku lura da irin ababen da za ku rika shiga da su kasar Saudiya - Gwamnatin tarayya ta gargadi 'yan Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwa kan adadin al'ummar Najeriya da ke zaman jiran a zartar masu da hukunci da kuma wadanda aka riga da zartar masu da hukuncin kisa a kasar Saudiya a sanadiyar laifuka na fataucin miyagun kwayoyi.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, gwamnati na neman a sassautawa al'ummar Najeriya hukuncin kisa da hukumomin kasar Saudiya suka zartar a kansu sakamakon laifuka na safarar miyagun kwayoyi da suka aikata.

Ku lura da irin ababen da za ku rika shiga da su kasar Saudiya - Gwamnatin tarayya ta gargadi 'yan Najeriya
Ku lura da irin ababen da za ku rika shiga da su kasar Saudiya - Gwamnatin tarayya ta gargadi 'yan Najeriya
Asali: UGC

Babbar mai bayar da shawara ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkokin kasashen ketare, Abike Dabiri, ita ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin wata hira da manema labarai na fadar shugaban kasa.

A ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin kasar Saudiya ta salwantar da rayuka bayan tabbatar da hukunci na haddin kisa kan wasu Maza biyu 'yan kasar Pakistan da kuma wata Mata 'yar kasar Najeriya sakamakon laifukan fataucin muggan kwayoyi da suka aikata.

A yayin da ba bu sassauci kasar Saudiya na ci gaba da zartar da haddin kisa kan masu aikata laifuka na fataucin miyagun kwayoyi, a halin yanzu kasar ta zartar da hukuncin kisa kan kimanin mutane 53 sakamakon laifin safarar miyagun kwayoyi da suka aikata cikin shekarar 2019 ta bana.

KARANTA KUMA: An yi garkuwa da Matafiya 37 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna

Hadimar shugaban kasa Buhari ta ce a halin yanzu akwai kimanin Mutane 8 da aka riga da zartar masu da hukuncin kisa yayin da kimanin 20 ke ci gaba da zaman a zartar masu da nasu hukuncin biyo bayan laifuka masu nasaba da haddin kisa da suka aikata.

Yayin bayyana takaicin ta dangane da kisan wata Mata 'yar kasar Najeriya biyo bayan hukunci na haddin kisa da aka zartar a ranar Litinin, Misis Dabiri ta gargadi al'ummar Najeriya da su lura tare da yiwa kawunan su karatun ta nutsu dangane da irin ababe da za su rika shiga da su kasar Saudiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel