Masana tattalin arziki na jaridar Daily Trust sun shawarci shugaba Buhari

Masana tattalin arziki na jaridar Daily Trust sun shawarci shugaba Buhari

Majalisar tattalin arziki ta jaridar Daily Trust, ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan daukan kyawawan matakai domin dawo da Najeriya bisa turba ta aminci wajen cire ta daga jerin kasashen duniya da ke sahu na gaba ta fuskar katutu na talauci.

Masana tattalin arziki na babbar jaridar sun shawarci sun shugaban kasa Buhari akan shimfida tsare-tsare cikin shekarar farko a wa'adin sa na biyu wajen tsarkake kasar nan daga kangi da kuma katutu na kuncin rayuwa mai hade da talauci.

Kungiyar zakakuran akan tattalin arziki ta shawarci shugaban kasa Buhari cikin wata sanarwa da sa hannun shugaban ta, Farfesa Ode Ojowu, da ya gabatar a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai a garin Abuja.

Masana tattalin arziki na jaridar Daily Trust sun shawarci shugaba Buhari
Masana tattalin arziki na jaridar Daily Trust sun shawarci shugaba Buhari
Asali: Depositphotos

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, majalisar masana tattalin arzikin ta yanke wannan hukunci yayin zaman da ta gudanar a ranar 30 ga watan Maris da manufa ta shimfida tsare-tsare da akidu na inganta tattalin arziki a wa'adin shugaba Buhari na biyu.

Majalisar ta bayyana rashin jin dadi dangane da yadda Najeriya ta kasance madubin talauci na dukkanin kasashen da ke doron kasa duk da albarkatun kasa da ta wadata da su ka ma da man fetur da ma'adanan sa da kuma albarka ta kasar noma.

Yayin shimfida shawarwari bisa ga na ta hangen nesan, majalisar ta nemi gwamnatin shugaban kasa Buhari ta kara kaimi wajen inganta harkokin noma, kananan masana'antu da kuma bayar da cin gashin kai ga kananan hukumomi a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Kiyasi: Tsawon rayuwar al'ummar Najeriya ba ya wuce shekaru 52 a doron kasa - Hukumar Kidaya

Ta kuma nemi shugaban kasa Buhari da ya sake zage dantse wajen tsananta tsaro musamman wajen kawo karshen ta'addancin masu garkuwa da mutane, rikicin makiyaya da manoma da ke haddasa karancin abinci.

Bayan neman hadin kai tsakanin fadar shugaban kasa da kuma majalisar tarayya wajen shigar da kasafin kudin kasa cikin doka a kan kari, Majalisar ta kuma bayar da shawara kan inganta ci gaban gine-gine da zai taimaka kwarai da aniyya wajen fidda kasar nan zuwa tudun tsira.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel