Rundunar 'yan sanda ta karayata labarin sace mutane 30 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Rundunar 'yan sanda ta karayata labarin sace mutane 30 a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Kaduna ta ce babu gaskiya a cikin wani labari dake kewaya a dandalin sada zumunta da wasu kafafen yada labarai a kan cewar an sace wasu mutane 30 a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

DSP Yakubu Sabo, kakakin rundunar a jihar Kaduna, ne ya karyata labarin sace mutanen a wata sanarwa da ya fitar yau, Talata, a Kaduna.

Sabo ya bayyana cewar hanakalin rundunar 'yan sanda ya kai kan labarin bogin da ake yada wa a dandalin sada zumunta a kan cewar an sace wasu mutane su 30 a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 1 ga watan Afrilu.

"Rundunar 'yan sanda na son sanar da jama'a cewar babu gaskiya a cikin labarin. Wasu marasa kishi ne suka kirkiri labarin domin tayar da hankalin matafiya da ke amfani da hanyar Abuja zuwa Kaduna domin gudanar da harkokin kasuwancinsu na halak.

Rundunar 'yan sanda ta karayata labarin sace mutane 30 a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Rundunar 'yan sanda ta karayata labarin sace mutane 30 a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Asali: Twitter

"Mutanen da ke yada labarin bogin sun canja gaskiyar abinda ya faru a ranar 1 ga watan Afrilu na kwace wata motar ma'aikatar shari'a kirar Hilux mai lamba CT 01 AF da wasu 'yan bindiga suka yi a kusa da Gidan Visa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da misalin karfe 6:30 na yamma. "yan bindigars sun raunata wani mutum mai suna Mshelia Sulaiman yayin kwace motar da sace mutanen cikinta.

"Tuni an tura rundunar 'yan sanda domin kubutar da mutanen da aka sace da kuma cigaba da gudanar da sinitiri a yankin," a cewar DSP Sabo.

DUBA WANNAN: Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Zamfara

Sannan ya cigaba da cewa, "mun samu wata takardar banki da ke dauke da sunan daya daga cikin mutanen da sace, kuma mun tafi da ita zuwa ofishinmu.

"Muna cigaba da binciken, kuma jami'anmu sun cigaba da farautar 'yan bindigar domin kama su da kubutar da mutanen da suka sace."

Rundunar 'yan sandan ta bukaci jama'a da su ba ta hadin kai ta hanyar basu muhimman bayanai da zasu taimaka wajen gano masu laifin cikin gaggawa da kuma dakile ragowar aoyukan ta'addanci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai (NAN) ya rawaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel