Abin na yi ne: An dakatar da zaman Majalisa saboda a karasa aikin kasafin kudi cikin makonni 2

Abin na yi ne: An dakatar da zaman Majalisa saboda a karasa aikin kasafin kudi cikin makonni 2

- Majalisar Dattawa tana so a tike aikin kasafin kudi a mako mai zuwa

- Bukola Saraki ya roki ‘Yan Majalisa su hanzarta da aikin da su ke yi

- Ana sa rai a mikawa Buhari kasafin kudin na bana a tsakiyar Afrilu

‘Yan majalisan Najeriya sun yi alkawari cewa za su kammala duk wani aikin da ya dace a kan kundin kasafin kudin bana nan da makonni 2 masu zuwa. A yau 2 ga Watan Afrilu, majalisar ta bayyanawa Duniya wannan a zaman ta.

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da bakinsa ya fito ya bayyana cewa za su yi kokari su karasa aikin kasafin kudi kwanan nan. Shugaban majalisar yake cewa za a karkare wannan aiki ne a Ranar 16 ga Watan Afrilun nan.

KU KARANTA: Abubuwan da Bukola Saraki ya fada a jawabin sa na Majalisa

An dakatar da zaman Majalisa saboda a karasa aikin kasafin kudi cikin makonni 2
Bukola Saraki ya na 'Yan Majalisa su hanzarta aikin kasafin kudin bana
Asali: Depositphotos

Bukola Saraki yayi kira ga kwamitin da ke aiki a kan kasafin kudin da su yi maza su kammala aikin su a Ranar Juma’ar nan. Haka zalika Saraki ya roki wannan kwamiti ta dawo ta gabatarwa majalisa duk aikin da tayi nan da mako guda.

Wannan ya sa aka dage zaman majalisar zuwa Ranar 9 ga Watan da ake ciki domin a bada dama ga shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya su gabatar da kasafin kudin su na shekarar nan a gaban Sanatocin kasar.

A daidai wannan lokaci ne kuma mu ke jin cewa Shugaban kasa Buhari ya sake fatali da wasu kudirorin da ‘Yan Majalisan kasar su ka kawo gaban sa. Hakan na nufin kudirorin Majalisa har 20 sun gaza samun shiga wajen Buhari a bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel