Mutuwa riga: Matashi ya nutse a cikin ruwa a jahar Kano

Mutuwa riga: Matashi ya nutse a cikin ruwa a jahar Kano

Masu iya magana suka ce tsautsayi baya wuce ranarsa, kuma dama ai mutuwa rigace, bata fita, kuma tana kan kowa, kamar yadda hakan ta tabbata akan wani matashi mai shekaru 20, Dayyabu Kashim a jahar Kano.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mutuwa ta riski wannan matashi ne yayin da yake shiga cikin wannan korama dake unguwar Dorayi, Ramin Kasa cikin karamar hukumar Gwale ta jahar Kano, yana wanka.

KU KARANTA: Majalisa ta yi watsi da kasafin kudin da Ministan Buhari ya mika mata

Kaakakin hukumar kwana kwana ta jahar Kano, Saidu Mohammed ya tabbatar da haka a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, inda yace wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu.

“Mun samu rahoton wannan lamari ne daga bakin wami mutumi mai suna Malam Mustapha Inusa da misalin karfe 2:25 na rana, inda yace ya hangi gawar Kashim ne yayin da take yawo a saman koramar.

“Samun wannan rahoto keda wuya, muka aika da jami’an hukumar kwana kwana zuwa koramar, suka isan bakin koramar da misalin karfe 2:36, koda jami’anmu suka isa, sun tarar da gawar matashin, inda muka mikashi ga ofishin Yansanda dake Dorayi.” Inji sji.

A wani labarin kuma, zababben gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nuna ma jam’iyyar PDP yatsa, tare da gargadinta game da abinda zai biyo baya idan har ta garzaya gaban kotu akan kalubalantar nasarar daya samu a zaben daya gudana makonni biyu da suka gabata.

Ganduje yace jam’iyyar PDP za tayi da-na-sanin kalubalantar nasararsa data shirya yi a gaban kotu, haka nan kuma wannan matakin da suke shirin dauka zai tarwatsa jam’iyyar kanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel