Yanzu-yanzu: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin yan ta’adda a Borno

Yanzu-yanzu: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin yan ta’adda a Borno

Rundunar sojin saman Najeriya, tace jami’anta masu gudanar da aikin Operation Lafiya Dole sun tarwatsa sansanin yan ta’addan Boko Haram a yankin arewacin Borno.

Air Commodore Ibikunle Daramola, Darektan sadarwa na rundunar ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gabatar a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu a Abuja, ya ce an gudanar da aikin ne a ranar Litinin.

Daramola yace duk da haka, rundunar ta tarwatsa wasu shuwagabannin kungiyar da mayaka a Magari da ke iyakar Chadi a yankin Arewacin Borno.

Ya bayyana cewa an samu nasara a aikin ne bisa labarin da rundunar ta samu daga rahotannin kwararru wanda yayi nuni ga cewa wasu manyan shuwagabannin ISWAP sun sauka a sansanin tare da wasu mayakanta.

Yanzu-yanzu: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin yan ta’adda a Borno
Yanzu-yanzu: Rundunar sojin sama ta tarwatsa sansanin yan ta’adda a Borno
Asali: Facebook

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya tace, Kakakin rundunar sojin yace, yin aiki tare da rundunar sama, zai kawo cigaban nasara a ayyukan tarwatsa yan ta’addan a yankin Arewa maso Gabas.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari ya sake fatali da wasu kudirorin ‘Yan Majalisa

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa rundunan sojin ruwa ta bayyana cewa zata gudanar da jarabawan daukar ma’aikata na shekarar 2019 a ranar 13 ga watan Afrilu a cibiyoyi 30 dake fadin kasar nan.

Kakakin rundunan sojin ruwa, Commodore Suleman Dahun ne ya bayyana haka a wani jawabi da yayi a Abuja.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel