Shugaban kasa Buhari ya sake fatali da wasu kudirorin ‘Yan Majalisa

Shugaban kasa Buhari ya sake fatali da wasu kudirorin ‘Yan Majalisa

Yanzu nan mu ka samu labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake yin watsi da wasu kudirori da-dama da ‘yan majalisar tarayya su ka aiko gaban sa da nufin cewa zai ratabba hannun sa.

Kamar yadda labari ya zo mana a yau 2 ga Watan Afrilun 2019, shugaba Buhari ya aikawa majalisar tarayya wasika a Ranar Talatar nan, inda ya bayyanawa Sanatoci abin da ya sa yayi watsi da wadannan kudirori da su ka kawo masa.

Daga cikin kudirorin da ‘yan majalisar su ka kammala aiki a kai, har kuma su ka nemi shugaban kasar ya sa hannu akwai kudirin Chartered Institute of Training and Development of Nigeria na 2018 da kuma wani National Housing Fund.

Bayan wannan kudiri da zai taimaka wajen samun kudin gina gidajen ma’aikata, akwai kuma wani kudirin da Buhari yayi watsi da shi wanda ake sa ran cewa zai taimakawa wajen karasa aiki a kamfanin Ajaokuta da aka dade ana zurawa ido.

KU KARANTA: Abin da Saraki ya fada wajen taron sababbin ‘Yan Majalisa a Abuja

Sauran kudirorin da shugaban kasar yayi fatali da su bisa wasu dalilai da ya bada a wasikar da ya aikawa Bukola Saraki sun hada da kudirin: Nigeria Aeronautical Research and Rescue da kuma National Institute of Credit Administration.

Shugaban majalisar dattawan kasar yace har wa yau, Buhari ya gagara sanya hannun sa a kudirin Federal Mortgage Bank of Nigeria da National Bio-technology Development Agency da aka gabatar a gaban sa a shekarar 2018 da ta wuce.

Hakan dai na nufin cewa a cikin shekarar nan kurum, Buhari ya ki sanya hannun sa a kan kudirori 20 da majalisa ta kawo masa da nufin cewa za su zama dokar kasa da za a rika aiki da su. A shekara 3 dai majalisar ta kawo kudirori 274.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel