Ana neman maida APC ta zama Jam’iyyar wasu shafaffu da mai a Najeriya – Okorocha

Ana neman maida APC ta zama Jam’iyyar wasu shafaffu da mai a Najeriya – Okorocha

Mai girma gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, wanda yake shirin barin kan karagar mulki, ya caccaki shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya da cewa yana kokarin kassara wasu a cikin APC.

Kamar yadda mu ka samu labari, Rochas Okorocha yayi wannan bayani ne Ranar Litinin, 1 ga Watan Afrilun 2019 lokacin da ya kai ziyara zuwa fadar shugaban kasa, Gwamnan yace Adams Oshiomhole yana ware wasu a jam’iyyar.

Shugaban gwamnonin APC na kasar ya zargi Oshiomhole da majalisarsa da kokarin maida mutanen Kudu maso Gabas saniyar ware a tafiyar APC. Okorocha yace bai kamata APC ta biyewa wannan kuskure na shugaban ta ba.

Fitaccen gwamnan ya koka da cewa a halin yanzu, APC ba ta da jiha ko guda a hannun ta a kaf shiyyar kasar Ibo, don haka yace idan za ayi wata ganawa na gwamnonin APC da shugaban kasa, za a ware daukacin mutanen Kudu ta Gabas.

KU KARANTA: Inyamurai su ka hana kan su samun mukaman Majalisa – APC

Ana neman maida APC ta zama Jam’iyyar wasu shafaffu da mai a Najeriya – Okorocha
Rochas Okorocha yace Oshiomhole ya kassara mutanen Yankin sa a APC
Asali: Depositphotos

Gwamnan mai harin zama Sanata ya bayyana cewa da gan-gan Adams Oshiomhole ya dage wajen ganin ya kassara mutanen Ibo karfi a jam’iyyar mai mulki. Sai dai duk da wannan, gwamnan yace bai samu wata matsala da shugaba Buhari ba.

Babban Gwamnan yace shugaba Buhari mutum ne mai hikima da hangen nesa, don haka ne ma da ya zo jihar Imo kamfe ya fadawa mutanen jihar su zabi wanda su ke so. A wancan lokaci APC da Okorocha tana rikici a kan kujerar Gwamna.

Okorocha ya ziyarci Aso Villa ne domin ya gayyaci shugaba Buhari zuwa jihar sa inda zai kaddamar da wasu tarin ayyuka da dama da gwamnatin sa tayi. Har gobe dai INEC ta hana gwamnan na Imo shaidar lashe zaben Sanatan jihar a APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel