Majalisa ta yi watsi da kasafin kudin da Ministan Buhari ya mika mata

Majalisa ta yi watsi da kasafin kudin da Ministan Buhari ya mika mata

Kwamitin majalisar dattawa dake kula da cinikayya da zuba jari ta yi watsi da kasafin kudin ma’aikatar cinikayya da zuba jari daya kai naira biliyan goma sha biyar da miliyan sittin da uku (N15,63bn), inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito majalisar ta dauki wannan mataki ne sakamakon bankado wani haramtaccen kamfani data yi wanda ma’aikatar ta sanya da nufin bashi kwangila, a yayin da Ministan ma’aikatar, Okechukwu Enelamah ya bayyana gabanta.

KU KARANTA: Hattara dai: Wasu mutane na kokarin kunna wutar rikici a Kaduna

Shugaban kwamitin, Sabo Muhammed ne ya bayyana haka a yayin zaman tantance kasafin kudin a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, inda yace basu da masaniyar wannan kamfani sakamakon baya cikin hukumomi 17 dake karkashin ma’aikatar.

Dan majalisa Sabo yace binciken da suka yi daga hukumar rajistar kamfanunuwa, CAC, ta nuna cewa wannan kamfani ba hukumar gwamnati bane, kamfani ne mai zaman kanta, tunda kashi 25 ne na gwamnatin tarayya, kashi 75 na mutane masu zaman kansu.

Don haka sai shugaban kwamitin ya nemi minista Enelamah ya aiko mata da cikakken bayani akan yadda aka saka kamfanin a cikin jerin hukumomin ma’aikatar, ma’aikatanta da kuma kasafin kudadenta na baya kafin yanzu.

Sai dai a nasa jawabin, minista Enelamah ya bayyana cewa a watan Mayu na shekarar 2018 ne gwamnati ta kafa wannan kamfani tare da amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma majalisar zartarwa.

“An samar da kamfanin ne don shiga hadin gwiwa tare da gwamnatin tarayya wajen samar da ayyukan more rayuwa, musamman manyan gine gine, ta yadda kamfanin zata zuba hannun jari wajen cimma wannan manufa ta gwamnati.” Inji minista Enelamah

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel