Da duminsa: PDP na kan gaba a ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar Rivers

Da duminsa: PDP na kan gaba a ci gaba da tattara sakamakon zaben jihar Rivers

Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa jam'iyyar PDP ce akan gaba a yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dawo da ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Rivers.

Jam'iyyar ta samu kuri'u 40, 197 a karamar hukumar Fatakwal, yayin da jam'iyyar AAC ta samu kuri'u 11866.

A karamar hukumar Ikwerre kuwa inda ministan zirga zirga, Chibuike Amaechi ya fito, PDP ta samu kuri'u 14,938 inda jam'iyyar AAC ta samu kuri'u 5,660.

KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa Burundi ta haramtawa Muryar Amurka da BBC aiki a kasar

A karamar hukumar Andoni kuwa wacce shugaban PDP na kasa, Uche Secondus ya taso daga cikinta, PDP ta samu kuri'u 92,056 yayin da AAC ta samu kuri'u 5335.

A karamar hukumar Oyigbo kuwa, jam'iyyar AAC ta samu kuri'u 32026, ita kuma PDP ta na kuri'u 8652 yayin da a karamar hukumar Eleme, jam'iyyar AAC ta samu kuri'u 2748, inda ita kuma PDP ta samu kuri'u 9560.

Cikakken labarin yana zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel