Yanzu Yanzu: Wike ya lashe kananan hukumomi 2 yayin da Hukumar INEC ke cigaba da tattara sakamoko

Yanzu Yanzu: Wike ya lashe kananan hukumomi 2 yayin da Hukumar INEC ke cigaba da tattara sakamoko

Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) na ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a jihar Rivers inda dan takaran gwamna, Nyesome Wike na jam’iyyar PDP ke kan gaba a kananan hukumomi biyu a birnin Port Harcourt da Ikwerre.

A yankin birnin karamar hukuman Port Harcourt, PDP ta samu kuri’u 40, 866 inda ta doke Biokpomabo Awara na AAC wanda ya samu kuri’u 11,866.

A yankin karamar hukumar Ikwerre, Wike ya samu kuri’u 14,938 inda ya doke Awara wanda ya samu kuri’u 5,660.

Yanzu Yanzu: Wike ya lashe kananan hukumomi 2 yayin da Hukumar INEC ke cigaba da tattara sakamoko
Yanzu Yanzu: Wike ya lashe kananan hukumomi 2 yayin da Hukumar INEC ke cigaba da tattara sakamoko
Asali: Depositphotos

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa rundunan yan sanda reshen jihar Rivers a ranar Litinin ta ce ta soma tura jami’anta zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe domin tsaron tattara sakamakon zabe da za a fara a jihar a ranar Alhamis.

KU KARANTA KUMA: Rivers: APC tayi ikirarin cewa babu rashin jituwa tsakanin Ameachi da Oshiomhole

Kakakin rundunan, DSP Nnamdi Omoni, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya fitar a Port Harcourt a ranar Litinin.

Hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) a ranar 21 ga watan Maris, ta bayyana cigaba da tattara sakamako da bayyana sakamakon a jihan tsakanin ranar 2 zuwa 5 ga watan Afrilu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel