An kama wani gwamna da laifin cin hanci

An kama wani gwamna da laifin cin hanci

- An kama gwamnan wata jiha da ya ke amfani da kujerarsa wurin aikata almundahana da shi da wakilansa

- An kama gwamnan sun hada baki da wani kamfani su na jigilar man fetur su na kuma raba kudin a junansu

A kasar Kenya, an kama gwamnan jihar Samburu, Moses Kasaine, bayan da babban mai shigar da kara Noordin Haji ya umarci kotu da ta tuhumi gwamnan, saboda kama shi da laifin cin amanar kasa da kuma yadda ya ke amfani da ofishinsa wurin biyan wasu bukatu na sa.

Har ya zuwa yanzu dai shi gwamnan da ake zargin da lauyoyinsa ba su ce komai ba game da zargin da ake yi wa gwamnan ba.

An kama wani gwamna da laifin cin hanci
An kama wani gwamna da laifin cin hanci
Asali: Facebook

A wani bayani da Mista Haji ya yi, ya bayyana cewa Mista Kasaine "ya na amfani da kujerar sa wurin yin kasuwanci da wani babban kamfani mai suna Oryx Service Station, wurin yin safarar man fetur tun daga ranar 27 ga watan Maris din shekarar 2013."

Kamfanin da ake zargin su na aiki tare da gwamnan ya karbi kudi kimanin naira miliyan 300, sannan gwamnan da wakilansa sun raba kudin a tsakaninsu.

KU KARANTA: 'Tun ina 'yar shekara 8 mahaifina ke kwanciya da ni'

Mai karar ya kara da cewa gwamnan har yanzu bai fito fili ya bayyana alakarsa da kamfanin Oryx Service Station ba, sannan kuma almundahanar da ya aikata ta sabawa dokar kasar Kenya.

Jihar ta Samburu ta na wurin arewa da yankin Rift Valley da ke kasar ta Kenya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel