Rivers: APC tayi ikirarin cewa babu rashin jituwa tsakanin Ameachi da Oshiomhole

Rivers: APC tayi ikirarin cewa babu rashin jituwa tsakanin Ameachi da Oshiomhole

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tace jawabin da Shugabanta na kasa, Adams Oshiomhole yayi cewa jam’iyyar bata da jam’iyyar siyasa da dan takara a jihar Rivers ba yana nufin akwai rikici a tsakaninsa da ministan sufuri, Rotimi Amaechi ba.

Oshiomhole ya bayyana haka ne akan umurni da tsohon gwamnan jihar Rivers yayi cewa masu biyayya ga jam’iyyar su zabi dan takaran gwamna a jam’iyyar African Action Congress (AAC), Awara Biokpomabo.

Jaridar Nigerian Tribune ta bayyana cewa an bayyana jam’iyyar APC da rashin cancanta wajen gabatar da yan takara a jihar Rivers kamar yanda kotun koli ta yanke hukunci.

Rivers: APC tayi ikirarin cewa babu rashin jituwa tsakanin Ameachi da Oshiomhole
Rivers: APC tayi ikirarin cewa babu rashin jituwa tsakanin Ameachi da Oshiomhole
Asali: UGC

A wani jawabin dauke das a hannun kakakin jam’iyyar, Lanre Isa-Onilu, ya zargi kafar watsa labarai da sauya jawabin da Oshiomhole ya yi don son zuciya.

KU KARANTA KUMA: Masarautar Saudiyya ta biya yaran dan jaridar da aka kashe makudan kudade – Rahoto

Ya kara da cewa Oshiomhole da Rotimi Amaechi na cin moriyar zumunci da martabar dake tsakanin su.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, rundunan yan sanda reshen jihar Rivers a ranar Litinin ta ce ta soma tura jami’anta zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe domin tsaron tattara sakamakon zabe da za a fara a jihar a ranar Alhamis.

Kakakin rundunan, DSP Nnamdi Omoni, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya fitar a Port Harcourt a ranar Litinin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel